Kano 2027 : Kamar A Hankali A Hankali Shugabancin Jam’iyya Na Karkata Ga Sanata Barau
Daga Abba Anwar
Da farkon farawa dai, nuna karkata ga bukatar wani ta siyasa, a ciki ko a wajen jam’iyyar siyasa, ko ma wacce ce, ina ga dama ce da yanayin tsarin dimukuradiyya ya ba wa kowa. Karkatar bukatar ya kasance ga wani mukami ne ko ga wata kujerar shugabancin jam’iyya ne ko ga wata dama cikin damammakin tsarin dimukuradiyya ne, duk abu daya a ke magana.
Misali, lokacin da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kusa karasa zangon mulkinsa na biyu, an samu wasu jajirtattu cikin masu ruwa da tsaki kan harkar jam’iyyar APC da su ka nuna zartaccen goyon bayansu ga mataimakin gwamna a lokacin, wato Abdullahi Umar Ganduje, kan bukatar a tsayar da shi takarar gwamna a lokacin.
Baya ga wadanda kuma ta karkashin kasa su ka dinga yin nasu kulle – kullen, daga masu son Gandujen da kuma wadanda suke da ra’ayin ba shi ya kamata a sa a gaba ba. Amma a lokacin an ga yadda jajirtattun yan gaba dai gaba dai, irin su shugabannin kananan hukumomi na lokacin su ka fito fili su na nuna goyon bayan su ga Ganduje.
Wannan ya faru ne karkashin shugabancin Murtala Sule Garo. Lokacin ya na shugaban karamar hukumar Kabo. Kuma a lokacin dai shine shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi 44 ta ALGON. Tun kafin maganar fitar da gwani na cikin gida ta taso a ka samu wadannan gwarazan su ka fito da bukatarsu. Haka nan an samu wadansu kungiyoyin da daidaikun mutane su na nuna goyon bayan su ga Ganduje a lokacin.
Ai cewa ma a ka yi, shi jagoran tafiyar, jagoran gwamnatin a lokacin, Kwankwaso ba Ganduje yake so ba. Amma kasancewar bukatar ta samu goyon bayan masu ruwa da tsaki, kuma haka Allah Ya kaddara, sai da ko ta dadi ko ta dole, APC din ta tsayar da Gandujen. Ko Kwankwaso ya so ko bai so ba, haka Allah Ya tsara abin zai faru.
Shigen kuma irin abinda ya faru kenan kafin Ganduje ya gama nasa zangon mulki na biyu, a ka dinga samun kungiyoyi da daidaikun mutane na kira kan takarar Garo, wasu kuma su na maganar tsohon mataimakin gwamnan Kano a lokacin, Nasiru Yusuf Gawuna, wasu kuma su na maganar AA Zaura wasu kuma su na maganar wasu wadanda tun farkon farawa ma sun san harkar da layin su ba ne. Saboda abubuwan da a ke iya gani a kasa baro-baro.
Allah cikin IkonSa da KaddararSa ya ba wa Gawuna da Garo tikitin. An ce a lokacin ba wanda bai dauka Garo ne zai samu ba. Ya na da shugabannin kananan hukumomi a hannunsa, a matsayin sa na kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi. An ce kuma ya na da goyon baya dari bisa dari na cikin gida. Baya ga yadda yake da alaka sama da kowa da shugabannin jam’iyya na kowane bangare. Tun daga Chapter, zuwa Ward zuwa karamar hukumar har zuwa matakin jiha. Amma da yake Allah bai sa shi ba ne, sai a ka hada shi da Gawuna a matsayin tikiti daya.
Ga dukkan mai hankali, ya kamata ya fahimci cewar haka Allah Yake aikinSa. Soyayya iya soyayya daga ciki da wajen jam’iyya a lokacin, ba wanda yake kusa da Garo. Daurin gindi iya daurin gindi a dukkannin yan takarar a lokacin, zan iya rantsewa da cewa wallahi ba wanda ya kama kafar Garo a tafiyar. Amman cikin tsari da Iko na Allah sai soyayyar ba ta kaddara zai samu ba.
To haka nan abin fa yake. Muddin soyayya ita kadai ba za ta iya bayarwa ba, to mai hankali ya kamata ya gane cewar kiyayya kuma ita kadai ba za iya hanawa ba.
Haka a kai tafiya daga wannan zango zuwa wancan zango. A dukkannin ragowar takarkarun haka abin ya kasance. Kuma kamar yadda tsarin neman maslaha yake da tagomashi kan yan takara, haka yanayin nuna goyon baya ga abinda mutum ke so kan yan takara yake da goyon bayan doka da kuma cikakken ikon da tsarin dimukuradiyya ya ba wa kowa.
Yanzu misali ai wasu sun fito sun nuna goyon bayan su kan mataimakin shugaban majalisar dattawa ta kasa, Sanata Barau Jibrin, a daidai kuma lokacin da wasu kuma ke nuna nasu goyon bayan ga tikitin Gawuna da Garo na 2023, da cewar a maimaita. Sannan kuma da tafiya ta yi tafiya sai wasu kuma suke nuna nasu goyon bayan kan cewa ya kamata a wannan karon shi ma Garo ya fito ya tsaya takarar gwamna ba takarar mataimaki ba.
A daidai ire-iren wadannan lokutan kuma, akwai masu hangen AA Zaura. Kuma su na fitowa su na fada a kunnen kowa. Akwai ma masu ganin cewa dan majalisar tarayya na Bichi, Abubakar Bichi, ya kamata shi ma ya fito, watakila zai iya zama raba-gardama. Kamar yadda suke hango masa.
To duk wadannan mutanen kowa ya na da damar ya fito ya fadi albarkacin bakinsa kan zabinsa na siyasa. Ba laifi ba ne. Misali ma bayan duk an gama maganar sasanci kan dan takarar gwamna, duk da haka idan akwai dan takarar da yake ganin hakan ba a yi masa adalci ba, zai iya fitowa ya ce bai yarda ba. Kuma dole jam’iyya ta ba shi damar gwada sa’arsa a yi zaben fidda gwani na cikin gida. Ai mun ga abinda ya faru da Sha’aban Ibrahim Sharada a 2023. Hakan kuma da ya yi ba laifi ba ne, akalla ya tabbatarwa da kansa cewar, shi fa mutum ne mai yanci, wanda tsarin dimukuradiyya ya ba shi damar yin abin da ya yi din.
Yanzu misali ai mun ga yadda wasu tsofaffin ciyamomi da tsofaffin kwamishinonin jihar Kano, su ka fara yin rubdugu wajen nuna goyon bayan su ga Sanata Barau. Duk da cewar daga baya wasu sun yi mi’ara-koma-baya sun ce ba da su a ka yi harkar ba. To a irin wannan tsari da a ke tafiya mai yanci, wadanda su ka ce ba da yawunsu ba, ai bai kamata a ga laifin su ba. Ita fa harkar nan zabi ce. Kowa ya na da cikakkiyar damar zabar abinda yake so. Kowa fa mai yanci ne. Tsarin ba fa na bawa da mai mallakar bawa ba ne. Babban abinda ya kamata kowa ya fahimta kenan, tun a na gane hanya. Ko mutum ya gane hakan dan kashin kansa, ko kuma duniya ta ganar da shi. Duk abinda mutum ya zaba ya na da yancin yin hakan, matsawar bai saba doka ba.
Tafiya kuma ta na tafiya, sai na ga an ce ga shugabancin “caucus” na kananan hukumomin Kano ta Arewa, karkashin shugabancin Inuwa Dan Shayi, wato mazabar Sanata Barau, sun kai masa ziyarar nuna goyon baya kan bukatar sa ta tsayawa takarar gwamnan Kano a shekarar zabe mai zuwa ta 2027. Ni a gani na yin hakan a wajen su ba laifi ba ne. Kamar yadda wasu ma su na da damar zuwa wajen wani su nuna goyon bayan su gare shi.
Ai mun ga yadda shugabancin mata na jam’iyya su ka kai ziyarar dunkulewa ga Abba Bichi kwanan nan. Ni a waje na ba laifi su ka yi ba. Tsarin da a ke kai ya ba su damar yin hakan. Tsarin ma ai ya ba shi kansa Abba Bichi dama da ya fito ya ce shi a kan kansa ya na goyon bayan takarar Garo. Kuma ya na da damar nuna cewar shi ma ya na da sha’awar tsayawa takarar gwamnan Kano. Duk ba laifi ba ne.
In dai har nuna goyon bayan takarar wani a cikin jam’iyya laifi ne, wanda ni a waje na ba laifi ba ne, ko kadan, to menene matsayin taron masu ruwa da tsaki da a ka yi na APC kwanan baya a Kano, har a ka ce APC gaba dayanta a Kano ta nuna goyon bayan ta a bayyane kan takarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a 2027?
Ni fa a waje na, babban abin lura shine, bai kamata wata bukata, duk girman ta duk kankantarta, ta rufe idon ta ga gaskiyar abinda ke faruwa ba, wato reality. Kamar yadda masu sauka daga mukamin da Sanata Barau ya ba su na mataimaka na musamman, suke da damar ajiye masa aikin sa, haka shi ma yake da damar ya rufe bakinsa ya yi shiru kar ya ce komai kan dukkannin fadi-tashin da a ke ta hakilo kan sa saboda wasu gungun jama’a sun fito sun ce su da shi mutu – ka- raba. Masu ajiye aikinsa sun burge ni. Dan kuwa su na da dalilansu. Tsarin da muke kai fa tsari ne mai yanci ga kowa da kowa.
Abinda nake kara kula da shi shine, yadda a gaba dayan wadanda su kai wa Sanata Barau caffa na “caucus” ba wanda Sanatan ya zama sanadiyyar samun wadancan mukaman nasu. A yadda na ji labari, in dai haka ne in kuma daidai ne, to lallai dole abubuwan da ke faruwa a kewayen Sanata Barau su zama ababen tsoratarwa da kuma fargaba. Labarin shine, na ji an ce, hatta a mazabarsa zuwa karamar hukumar sa zuwa yankin sa har zuwa jiha, ba shi da ko da mutum daya a cikin shugabancin jam’iyyar APC a Kano din.
Sa’annan kuma abinda ya sa na ke cewa kamar dai shugabancin jam’iyyar APC din ya na karkata zuwa ga Sanata Barau, wajen ba shi goyon baya shine, yadda na samu wasu labarai na karkashin kasa cewa wasu gungun shugabannin jam’iyyar daf suke da su kawo masa tasu caffar. Babban abin tambaya a nan shine, wai kuwa idan har yadda abubuwan dake faruwa su ka ci gaba da tafiya a haka, me hakan yake nunawa kuwa?
Babban abinda na sani shine a cikin shugabanni da mabiya, akwai wadanda sun yarda Allah ne Ke yi ba wani ba. A cikin manyanmu kuma jiga-jigai da suke da wannan tawakkali da zartaccen imani kan hakan, har yanzu mutane biyu kacal na sani da suke kan hakan. Bayan su ban ga wani ko wata ba. A nawa hangen da nawa lissafin fa na ce. Zan iya daidai zan iya kuskure. Amman nan gaba jama’a za su gano da wa da wa nake nufi suke kan hakan.
Ni dai babbar shawara ta ga Sanata Barau ita ce, kamar yadda a ka san ka da kawaici da kaskan-da-kai da nuna komai ba komai ba ne, to idan ka ci gaba a haka, tabbas goben ka za ta yi kyau.
Kuma yafiya da tausayawa lokacin samun nasara dabi’un manyan mutane ne.
Anwar ya rubuto wannan daga Kano
Talata, 9 ga watan Disamba, 2025
