Ban Taba Nadamar Aiki Karkashin Ganduje Ba – Abba Anwar
Wannan rubutun nawa dan somin tabi ne na bayani game da yadda na yi aiki a karkashin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje CON, a matsayin babban sakataren yada labaransa (Chief Press Secretary, CPS) .
Akwai tarin bayanai na nan zuwa nan gaba cikin wani littafi da nake rubutawa kan yadda na yi wancan aikin tare da shi.
Da farko ina son bayanin cewa, ni fa ban taba nadamar aiki da Ganduje ba a matsayin mai magana da yawunsa, a cikin shekaru shida da na yi a wannan aiki. Daga 2018 zuwa 2023. Ina yin wannan bayanin ne ga masu sha’awar ji da kuma ‘yan gaza gani da masu yaudarar kai. Har ma da wadanda su ba su ma san me suke so ba a irin wannan tattaunawa.
Dole na kasance cikin nishadin ganin a lokacin da nake matsayin mai magana da yawunsa jihar ta samu ci gaba a bangarori da yawa. Kafin na tabo wannan bangaren ma tukuna, a kashin gaskiya na karu da abubuwa da yawan gaske daga fagen kwarewarsa kan aiki. Kasancewarsa na daya a duk fadin jihar ta mu mai albarka.
Babban abin jin dadin kuma shine, a daidai lokacin da nake aiki a tare da shi, a daidai lokacin kuma ina yi wa jihata hidima ne kai tsaye. A wannan mukamin ne na kara fahimtar alakar da ke tsakanin aikin jarida da gwamnati. Ba a matsayin karatu a takarda ba kawai.
Na yi alfahari da yadda gwamnatin sa ta samar da tsaro mai inganci. Wanda ta haka ne a ka samu fahimtar juna tsakanin jami’an tsaro na bangarori. Tabbas an inganta tsaro a lokacin mulkin sa. Fiye da yadda jihohi suke da dama a lokacin. Balle a wannan lokaci da tsaro ya zama tamkar azurfa ko turare dan goma. Gwamnatin sa ta yi hobbasa mai inganci.
An inganta tsaro ta fuskoki da dama a zamanin Ganduje a jihar Kano. Wannan tabbataccen abu ne da ba ya bukatar wani dogon sharhi.
Haka nan kyakkyawar mu’amalarsa da mutane ta kara min kwarin gwuiwar bude ido na in kara nazartar harkokin zamantakewa da alakantuwa da juna tsakanin muki da bagarorinsa da kuma yadda a ke tafiyar da shi kan sa mulkin. Sannan a daidai lokacin na kara nazarta gami da sanin ta yaya masu kula da harkokin hulda da jama’a na yau da kullum, suke aikinsu a matsayin tsintsiya daya madauri daya.
Daga cikin muhimman abubuwan da na koya a wannan aikin nawa shine, yadda alaka ke tsakanin masu kula da bangaren jarida da hulda da jama’a suke da iyayen gidansu, da suke wa aikin bayan barin mulki. Babban wanda ya fi cancanta da in bayar da misalinsa shine Farfesa Sule Ya’u Sule. Wanda ya rike mukamin Daraktan Yada Labarai a gwamnatin soja da ma ta farar hula. Lokacin tsohon gwamna, Malam Ibrahim Shekarau.
Na koyi abubuwa da yawa daga wajen sa na yadda zan rike aiki na da nagarta. Haka nan na kara koyon yadda yanayin aikin yake daga wajen Baba Halilu Dantiye (mni). Wanda shi ma ya yi irin aikin a lokacin gwamnatin tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso.
Dabarar da Allah Ya kimsa min ita ce, na kan tuntube su saboda na samu daidaito kan yadda aikin yake. Ni fa a lokacin ba na yi wa kaina kallon dan siyasa. Illa iyaka kawai ina yi wa kaina kallon dan jarida kuma mai aikin jarida.
Wanda a lokacin babban buri na kawai shine, na kare mutuncin aikin. Tare da kare kimar wadanda na fito daga cikinsu. Wato yan jaridar mu dake karkashin kungiyar mu ta yan jarida ta kasa, wato NUJ.
A dalilin yadda na tsinci kaina a matsayin babban sakataren yada labarai na gwamna Ganduje, sai na kara samun damar fahimtar yadda siyasa take ko yadda a ke amfani da siyasa wajen aikin jarida. Ba fa ina nufin yadda ilimin sadarwa tsakanin al’umma yake ba, kamar yadda a ke koyar da shi a jami’o’inmu ba. Ina nufin yadda wadanda ya kamata a ce su ne kan gaba wajen kare kima da mutuncin aikin, su ka kasance su ne kuma suke yi wa aikin kanshin mutuwa.
Yadda har lalacin da lalacewar ta kai ba sa iya ma tabuka komai har abin ya shafi irin sakamakon da aikin nasu ke fitarwa. In takaice wa mai karatu bayani, sai da ta kai fa, hatta daga cikin kananun abubuwan da masu rike da irin wadannan mukamai ke yi, na rubuta bayani/sanarwa/takarda ga yan jarida wato (press release) za ka iske ba a ma iya rubutawa ba.
Watakila mai karatu ba zai gane me nake cewa ba sosai, har sai ya dauki ire-iren wadannan “press releases” da irin wadannan mutane su ka rubuta, ya danganta su da ire-irensu da suke fitowa daga hukumar yan sanda ta kasa (Police) ko daga fadar gwamnatin tarayya (Presidency) ko daga ma’aikata mai hankali da tsari, ya ga banbancin dake tsakanin su. Za ka gane banbancin shiririta da ingantaccen aiki.
Ai sai da na rike wancan mukamin sannan na fahimci cewar sau da yawa wadanda a ke dauka a matsayin kwararru a harkar yada labarai a gwamnatoci, su suke angiza irin wadannan gwamnatocin cikin ramin kare-kukanka. Sau da yawa za ka tsammaci kwararru ne sun san me suke yi. Amma ina ashe ta-gina-ne-ba-ta-shiga-ba. Jahilci da kafafunsa.
Lokacin da nake CPS na Ganduje ya ba ni duk damar da ta kamata na yin aiki ba tare da katsalandan ba. Hakan ya ba ni dama na yi aiki na bisa tsarin ka’idar aiki ba bisa lusaranci ba.
A lokacin dukkan umarnin da nake samu ina samu ne kai tsaye daga gwamna. Ba daga wani dan majalisar zartaswa ko daga wani babban jami’i na gwamnatin ba. Ba kuma daga wajen iyali ba. Hakan ya matukar ba ni damar yin aiki na a tsaftace. Kuma a kan haka na tsaya a cikin shekaru shidan da na yi a matsayin CPS.
Har yanzu dai kamar yadda na ambata a bisa, ban taba nadamar ina cikin gwamnatin Ganduje a ka samu abubuwan more rayuwa na ci gaban kasa a Kano ba. Har yanzu ina alfahari da manyan gadojin sama da na karkashin kasa da a ka samu. Tare da gina asibitin zamani mai kula da masu cutar daji (Cancer Centre).
Sai kuma karasa aikin katafaren asibitocin nan na Muhammadu Buhari dake Giginyu da kuma asibitin yara, Halifa Isyaka Rabi’u, dake kan Zoo road. Ga kuma gine-ginen manyan asibitoci da a ka samar a hedikwatar sabbin masarautu guda hudu da a ka yi. Da sauran abubuwan bila-adadin.
Ni fa a waje na, har yanzu har zuwa gobe, abin alfahari ne sabbin masarautu hudu da a ka yi a lokacin gwamnatin Ganduje. An yi ne dan kara habaka da cigaban al’adunmu. Faqad.
Advertisement
Bisa la’akari da abubuwan da na lissafa din nan da a ka yi a lokacin gwamnatin Ganduje, ta yaya wani zai bude dogon bakin sa ya ce wai ga wani lokaci da Abba Anwar ya yayyaga gwamnatin Ganduje da sunan wai bai yi komai ba? Irin wannan tunani, ba kawai yaudarar mai karatu ba ne, wannan jahilci ne da kin gaskiya baro-baro.
Kamar dai yadda har yanzu ba na nadamar aiki karkashin Ganduje, har yanzu ina da masaniyar cewa babu wata gwamnati da ba ta da irin nata kura-kuran. Tun daga lokacin da a ka kirkiri Kano a matsayin jiha, tun daga mulkin soja da na farar hula, har kawo yanzu da Abba Kabir Yusuf ke rike da gwamnati, babu gwamnatin da ba ta da nata kura – kuran. Wannan shine matsayata. Ya rage ga ‘yan taratsi ko munafukai su fahimci duk abinda suke ganin ya yi musu daidai.
A saboda haka, na ƙalubalanci kowane irin mutum da yake tunanin ya fahimci mecece gwamnati ko yake tsammanin shi kadai ya san harkokin yau da kullum na gwamnati, ko ya dauka cewar shi ya yi nisa kan yadda aikin jarida yake, da ya kawo min sakin layi (paragraph) daya jal, ko wata jimla, wacce na rubuta a yayin ina CPS a gwamnatin Ganduje, wacce na yi watsi na kuru-kuru mara kan gado, ga gwamnatocin baya na Kwankwaso ko na Shekarau.
Kai ba ma wannan ba, a kawo min sakin layi daya ko wata jimla ta baro-baro mara kan gado da na yi watsi da ayyukan gwamnatin da ta biyo bayan sauka ta daga kan kujerar CPS din. Har fa a gwamnatin Abba Gida Gida nake nufi. Balle ma wai a ce a gwamnatin da na yi aikin CPS a ciki, ta Ganduje. A ina na taba jefa kai na cikin irin wannan hayagagar mara kan gado? Ni yin haka ba dabi’a ta ba ce ban san ta ba.
Ina sauraren hakan cikin gaggawa!
Ni ban samu irin wannan horaswa ba. Ni an horar da ni ne in zama dan jarida ba dan gwagwarmayar kungiya ba. Kuma dukkan shekarun aiki na su na nuni da hakan. Har kawo lokacin da na yi aiki da Ganduje a matsayin CPS.
Abba Anwar
