APCn Kano Cikin Sarkakiyar Dimauta : Yayin Da Kulle-Kulle Kan DSP Barau Ke Kara Ta’azzara
Daga Abba Anwar
Ni fa a tawa fassarar ta kashin kaina, duk rigingimun da ke faruwa a cikin jam’iyyar APC a jihar Kano, kar ka raba daya biyu, akwai sakaci da rauni da son zuciyar shugabanci. Ta ma kowane bangare ka kalli me a ke nufi da shugabanci.
Samun iko da tsayawa kan magana daya da kuma daukar dukkannin wadanda ke kasan ikon mutum a matsayi daya, a matsayin sa na shugaba, shi a ke nufi da sahihin shugabanci. Wanda ba karkatacce ba. Idan sama, wato kai ya gyaru ya zama mai inganci, to dole kuwa ka samu ragowar sassan jiki sun gyaru su ma.
Wani abinda har yanzu shugabanni da dattawa da mabiya ba su bayar da hankalin su kan sa ba shine, shi fa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, bukatar kashin kansa, a wajen sa, gaba take da bukatar kowa. Duk girmansa duk kankantarsa. Kuma a kowace jiha yake.
Da zarar a ka kara matsawa gaba, sai Tinubu ya fahimci cewa APCn Kano, wacce a ka mayar dandalin baje hajar son zuciya da son rai, taron kwaram da hama ne, to wallahi yin “waje rod” da dukkan wadanda ke tunanin su ne APC a Kano, shi ya fi masa sauki kan cire hular dake kansa.
Shi kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I Jibrin, CFR, har yanzu abokan adawarsa na gaske, da yawa daga cikinsu, da kuma makiyansa na gaske da yan hassadarsa na gaske, sun kasa gane yadda Allah ke masa a yanayin siyasar jihar tamu ta Kano.
Labarin da na samu na baya bayan nan kan irin makircin da a ke kulla masa shine, an ce a na nan a na shirya yin taron manema labarai, dan yin kira ga majalisar dattawa da kuma fadar shugaban kasa, wai a yi gaggawar cire shi daga mukaminsa. Sannan kuma an ce za a je majalisar dattawan dan yin zanga-zanga ta musamman ai kira ga majalisar da ta yi gaggawar cire shi daga mukamin sa.
Ni abinda ya ma ban dariya shine, to su masu wannan niyyar su ma yan kishin Kano ne ko kuwa? A baya an sha yin zargi kala – kala a na cewa Sanata Barau ya zamewa wasu masu mukamin gwamnatin tarayya da kuma wasu da a ke son ba su mukamai, kadangaren bakin tulu. A kai ta shirya labaran da da na yanzu kala-kala a na sukar sa gami da cin zarafinsa. Wai, a cewar su, Sanatan ba ya kishin Kano. To su yanzu kishin Kanon ne ya sa suke shirya wannan abin?
Kuma wani babban abin mamaki shine, yadda ire-iren wadancan mutanen ke rufe ido kan irin ayyukan raya jiha da wannan bangare namu da Sanata Barau ya dukufa ya na yi. Shi dai na farko ba “local champion” ba ne. Kwararren dan siyasa ne. Wanda kuma idonsa ya bude ga yanayin siyasar kasa. Har ma da siyasar nahiyar Afirka da duniya gaba daya.
An manta da yadda Sanata Barau ke daukar nauyin karatun mutane a fadin jihar Kano. A manyan makarantunmu na cikin gida. Da kuma jami’o’in kasashen waje. An manta da kokarin da ya yi wajen kawo jami’a sukutum guda a yankin sa na Kano ta Arewa. Wato Federal University of Science and Technology, Kabo.
Ga kuma hukumar raya yankin arewa maso yamma (North West Development Commission), dan ci gaban wannan yanki namu. Ga kokarin da yake wajen inganta harkar tsaro a wannan jiha ta mu. Baya ga motocin aiki da babura da kayan aiki na daruruwan Milyoyin Naira, da ya rarraba ga hukumomin tsaro, musamman hukumar yan sanda ta kasa, reshen jihar Kano. Ga kuma tallafi da yake bayarwa tun daga mazabarsa har zuwa ga al’ummar jihar Kano gaba daya, na kara habaka rayuwar su ta yau da kullum.
Wani abu kuma da a ke mantawa shine, irin yadda kowane lokaci a ke cewa shine ya hana a ba wa wane mukami ko shine ya yi kullin da a ka dawo da wane, a irin hakan fa kuma, akwai masu ganin cewa in dai har Sanata Barau ya na da irin wannan dama, to lallai kuwa ya zama jan-wuya. Akwai masu irin wannan tunanin cewa in dai kuwa haka ne, to lallai Sanata ya zama kai-kadai-gayya.
Ni dai babban jan hankali na ga shugabanni da dattawa da mabiya da dukkannin masu neman wani mukami da gaske ko da gangan da kuma yan gutsuri-tsoman jam’iyya da kuma wadanda ke kadawa kansu kararrawa ko masu sa ganye a jikinsu na kowane irin mataki, a matsayin su haja ne na sayarwa, da kuma yan in ta yi ruwa rijiya in ba tai ba masai, ya kamata su gane cewar, a wannan zamani da siyasa ke kara bude cikin ta, zamanin yancin kai a ke a harkokin jam’iyya. Kowace jam’iyya ce ma kuwa ba wai lallai APC ba. Ba wanda ya isa ya ce ya mallaki mutane a matsayin bayi. Yanci, yanci, yanci kawai!
Kukan kurciya jawabi ne!
Anwar ya rubuto wannan daga Kano
Talata, 16 ga watan Disamba, 2025
