Sanata Barau Ya Yi Wa Sabuwar Shekara, 2026, Lale Da Gurbin Aikin Gwamnatin Tarayya 129 Ga Mutanensa
Daga Abba Anwar
Ranar Alhamis da sabuwar shekarar 2026 ta shigo ne, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na Kasa, Sanata Barau Jibrin ya yi rabon takardun daukar aiki a gwamnatin tarayya guda 129 ga mutanen sa.
Ni dai har zuwa yanzun nan da nake rubuta wannan ban gani ko jin labarin wani dan siyasar da ya yi wa 2026 irin wannan lale ba, ba ma a jihar Kano ba, a Arewacin kasar nan. Ko ma a cikin kasar. Har yanzu ban ji ba ban gani ba. In akwai kuma a sanar da ni.
Shi din dai ya kasance dan siyasa daya tilo da ya yi irin wannan gagarumar hobbasa a ranar farko ta shigowar sabuwar shekara. Wannan ba abu ne da a ka yi shi a boye ba. An yi shine a bainar jama’a.
Karamin Ministan Gidaje, Hon Yusuf Abdullahi Ata ne ya wakilci Sanatan a wajen wannan gagarumin taron rarraba takardun aikin. Tare da rakiyar wasu mukarraban Sanatan.
Irin wannan aikin ba daga yau ya fara ba. Dama dabi’arsa ce tallafawa mutane ta irin wannan hanya. Wato shi ba kawai rabon kifi yake ba, a’a ya na nunawa mutane yadda a ke kama kifin. Kamar yadda wata karin maganar mutanen Sin (kasar China) ke cewa.
Kowa dai ya san yadda samun aiki a gwamnatin tarayya ke da dan karen wahala. Amma cikin Ikon Allah, sai ga shi ya samo wadannan gurabe har 129. Kai da gani ka san wannan aiki ne kawai daga Allah.
Irin wannan kokarin kuma shi yake nunawa mutane yadda Sanatan ke kishin mutanen sa. Ya yarda da aniyar cewar ya kamata mutane su zama masu dogaro da kai. Kuma babban abin ban sha’awa shine, hanyar da a ka bi wajen tantance wadannan mutane. Komai a bude ba nuku-nuku. Ba fifita wasu mutane a kan wasu.
Wato yadda wannan shekara ta 2026 ke dauke da ba-zata kala-kala a tafiyar siyasar wannan kasa, bisa ga irin labaran da suke iske wadanda ke da kunnen jiyo irin labaran, akwai dukkan alamu cewa Juma’ar Sanatan za ta yi kyau.
Mutumin da a ranar farko ta sabuwar shekarar 2026 ya farantawa iyalai har 129, baya ga masoyansu da yan uwansu, ai kuwa wannan mutumin ya cika gwarzo mai kwazo da kishin jama’arsa. Larabar bawan Allan nan ta yi kyau tun ma farkon shekara, balle a nitsa ciki.
Shi Sanata Barau ba wai maganar aikewa da sakon sabuwar shekara ba ne a ransa. A’a shi maraba ya yi da shigowar sabuwar shekarar da guraben aiki a gwamnatin tarayya ga mutane 129. Sannu da aiki jarumi. Mutum daya tilo dan baiwa.
Shi fa Sanata Barau sunansa kawai, ya na nuni ga jajircewa, kishin al’ummar sa, tallafawa rayuwar al’umma, wayewa, sanin makamar aiki, budaddiyar manufa, budaddiyar zuciya, kyakkyawar shimfidar fuska da kuma shugabanci nagari.
A matsayin sa na daya daga cikin jagororin jam’iyya mai mulki ta APC a matakin kasa, shi fa ya yarda da cewar matsawar a na son ci gaban al’umma, to dole a tallafi rayuwar su. Tallafa mai ma’ana mai cike da girmama dan Adam da sanin kimar mabiya. Shi ya sa ma ya yi fice mai ma’ana tsakanin tsararrakinsa. Ba ma maganar na baya a ke ba tukuna.
Anwar ya rubuto wannan daga Kano
Lahadi, 4 ga watan Janairu, 2026
