Nuni Ga Fifikon Sanata Barau Yayin Babban Taron Kasa na APC
Daga Abba Anwar
Yayin da a ka yi Babban Taron Kasa na jam’iyyar APC a filin Eagle Square da ke Abuja, a gaban Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tare da dukkan manyan jiga-jigan APC a ƙasar, da kuma wakilai daga jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja, an tsara cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, CFR, zai kasance cikin kaɗan daga cikin waɗanda aka zaɓa domin gabatar da kudurori kan harkokin gudanarwa, tsari da ci gaba na jam’iyyar a lokacin taron.
Kudurorin da manyan shugabanni suka gabatar, irin su Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, GCON da Kakakin Majalisar Wakilai Tajuddeen Abbas, GCON, sun haɗa da rushe shugabancin jam’iyyar na yanzu da sauran batutuwan da suka shafi ci gaba da tafiyar da jam’iyyar.
A ƙarƙashin wannan gagarumin tsari a ka ba shi Sanata Barau damar gabatar da muhimmin kuduri na tsawaita wa’adin kwamitocin riƙo na shugabancin jam’iyyar a jihohin Ekiti da Osun.
Sanatan ya fara da gabatar da kansa cikin sauƙi da tawali’u, inda ya yi alfahari da asalin sa, inda ya ce “Sunana Barau I. Jibrin, mamba na APC a mazabar Kabo, ƙaramar hukumar Kabo a jihar Kano.”
Jawabin da ya yi wajen sauke nauyin da a ka dora masa a wajen taron, ya nuna yadda yake da zurfin fahimta a harkar dimokuraɗiyya. Maganganunsa sun bayyana cikakkiyar fahimtarsa game da tsarin jam’iyyar APC da yadda a ke tabbatar da dorewar jam’iyya a kowane mataki.
Ya ce “Kudurina shi ne, Ina gabatar da wannan kuduri na gaggawa bisa buƙatar gudanarwa da tsari, dangane da shugabancin jam’iyyar APC a jihohin Ekiti da Osun.
Jam’iyyar a yanzu tana aiki ta hannun kwamitocin riƙo da a ka nada a matakin mazabu, ƙananan hukumomi da jihohi a jihohin Ekiti da Osun. Wa’adin wadannan kwamitoci zai ƙare a ƙarshen watan Maris, 2026.”
Ya ƙara da cewa “Kwamitocin riƙon su na cikin wa’adinsu na tabbatar da tsari, ci gaba da ayyuka da kuma daidaita al’amuran jam’iyya a waɗannan jihohi.”
Don nuna cikakken fahimtarsa ga harkokin siyasa, ya bayyana dalilan da suka sa a ka nemi kara musu wa’adin, yayin da ya ce “Irin halin da ake ciki a jihohin Ekiti da Osun, musamman yanayin dumamar al’amura da ke tattare da zaɓukan gwamna masu zuwa, sun haifar da yanayin da bai ba da damar gudanar da zaɓukan shugabancin jam’iyya cikin lumana da kyakkyawan tsari ba.”
Ya ci gaba da cewa “Ya na da muhimmanci ga muradun jam’iyya a tsawaita wa’adin kwamitocin riƙo domin ba su damar tsara abubuwa yadda ya kamata, ƙarfafa tsarin jam’iyya da kuma shirya gudanar da zaɓukan shugabancin jam’iyya.”
Ya kuma yi nuni da Sashe na 13(1) na kundin tsarin APC wanda ya ba da wannan damar. Dan a nunawa kowa cewar, ita fa jam’iyyar mai tsari ce.
Kudurinsa ya ƙunshi sassa huɗu, yayin da ya ce “Ina gabatar da cewa wannan Babban Taro na Kasa ya:
(i) amince da tsawaita wa’adin kwamitocin riƙo a matakin mazabu, ƙananan hukumomi da jihohi a Ekiti da Osun,
(ii) tsawaitawar za ta kasance na tsawon watanni 6 daga ƙarshen Maris 2026 zuwa ƙarshen Satumba 2026,
(iii) a bai wa sassan jam’iyya dama su yi amfani da wannan lokaci wajen kammala shirye-shiryen zaɓukan shugabannin jam’iyya,
(iv) a kuma buƙaci dukkan ‘ya’yan jam’iyya su ba da haɗin kai ga kwamitocin riƙon. Wannan kuduri an gabatar da shi ne domin haɗin kan jam’iyya, ci gaba da gudanarwa da kuma tabbatar da tsari.”
A matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar, fitowarsa a matakin ƙasa na ƙara ƙarfi. Nutsuwarsa, basirarsa da zurfin fahimtarsa sun nuna yadda yake daraja dimokuraɗiyya da ƙa’idojinta. Jawabinsa ya nuna ƙwarewa da fahimtar siyasar jam’iyya sosai.
Jinjina gare shi, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa— abin alfaharinmu, shugaba na gari.
Anwar ya rubuta daga Kano
Lahadi, 29 ga watan Maris, 2026


