Close Menu
  • Home
  • Business
  • Health
  • News
  • Politics
  • Security
  • More
    • Arts and Culture
    • Environment
    • Lifestyle
    • Opinion
    • Social Issues
    • Sports
    • Travels
  • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram
FINENEWS NIGERIAFINENEWS NIGERIA
  • Home
  • Business
  • Health
  • News
  • Politics
  • Security
  • More
    • Arts and Culture
    • Environment
    • Lifestyle
    • Opinion
    • Social Issues
    • Sports
    • Travels
  • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
FINENEWS NIGERIAFINENEWS NIGERIA
Home » DSP Barau Da Akpabio Kan Sambatun Trump : Jajirtaccen Shugabanci Da Tsoron Allah

DSP Barau Da Akpabio Kan Sambatun Trump : Jajirtaccen Shugabanci Da Tsoron Allah

By EditorNovember 5, 2025 Opinion
Facebook Twitter LinkedIn Email WhatsApp
FB IMG 1762347946522

DSP Barau Da Akpabio Kan Sambatun Trump : Jajirtaccen Shugabanci Da Tsoron Allah

Daga Abba Anwar

Babban abin alfahari da sowa da ya same mu, mu mutanen Kano shine yadda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Kasa, Sanata Barau Jibrin ya yi kiki- kaka da Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio, kan sambatun wai kisan kiyashi da shugaban Kasar Amurka, Donald Trump a ka ruwaito cewar ya ce, a na yi wa mabiya Addinin Kiristanci a wannan kasa ta Najeriya.

Lokacin da Akpabio ke kakkaucewa yin maganar a zauren majalisar, shi kuma Maigirma Sanata Barau, ya dage cewar bai kamata a ki cewa komai kan batun ba. Nan fa a kai ta takaddama a idon duka ‘yan Najeriya dama idon duniya.

Daga cikin darussan da wannan takaddamar tsakanin Shugaban Majalisa da Mataimakin sa ke nunawa akwai, fahimtar waye Sanata Barau wajen jajircewa da kin cin amanar mutanen sa, a harkar shugabanci.

Wannan abu ya kara nunawa kowa cewar, shi fa Sanata Barau da Allah Kadai ya dogara. A harkar sa babu batun jin tsoron wani abin halitta. Dan kuwa an ji ya ce “Ni fa ba na wani jin tsoron Trump!

A wannan sauke nauyi da Sanata Barau ya yi, ya kara nunawa mutanen jihar Kano cewar shi fa ba mutum ne da idan an sa shi a gaba zai ci amanar mutane ba. Ba kuma mutum ne da a ke tunanin wani ko wasu za su juya shi bisa son zuciya ba. Mu na da irinsa amma daidaiku a jihar Kano.

Wannan abinda ya faru kuma, ya kara nunawa kowa cewar, shi fa Sanata Barau ya fi fifita tsoron Allah da amana da jajircewa kan abinda mutanen sa ke so, kan tsoron wani dan Adam. Ba a kasar nan ba, ko ma a matakin duniya ne.

Tun tasowar wannan zancen fankan-fayau na Trump, akwai mutane biyu zuwa uku da su ka burge ni wajen mayar da martani kan wannan abu.

Daga ciki akwai wani Megidana kuma Ogana, tsohon Janar na Soja, General Ishola Williams, a wani shiri na gidan talabijin na Channels, a wani shirinsu mai suna “Inside Source.” Shi a cewarsa ma “Shugabannin Kiristoci ne ke matsawa Amurka lamba, sai ta sa wa Najeriya takunkumi.”

Ya ce “Christian Clerics Pushing US To Sanction Nigeria.” Ina rokon mai karatu da ya je ya lalubi wannan hira ta Gen Williams a YouTube.

Akwai kuma Barrister Bulama Bukarti, dan Najeriya mazaunin Ingila, da a ka yi hira da shi a gidan talabijin na CNN. Wallahi idan ka ji hirar za ka ma gane, ba wai maganar da Trump ya yi ta son zuciya ce kawai ba, a’a za ma ka gane cewar akwai ainihin jahilcin yanayin da a ke ciki daga bangaren Trump din.

Shi fa Bukarti rubutun da ya yi kan Digirinsa na Uku, PhD, ya yi shine fa kan abubuwan da kacokan su ka shafi Boko Haram. To ka ga kuwa me za a layance masa a harkar? Shi ma ina rokon mai karatu da ya je ya binciko hirar da CNN din ta yi da Barrister Bukarti.

Kuma fa wani abinda zai ba ka sha’awa shine yadda daga baya Akpabio ya tambayi ‘yan majalisa cewar, wai ku na so a tattauna maganar Trump a zauren majalisa? Gaba dayansu su ka ce su na so. Ka ga kenan gaba dayan su abinda Sanata Barau ke so kan a tattauna maganar Trump, su ma a kan haka suke. Barau Ajiyar Allah!

Ga fa yadda takaddamar ta kasance tsakanin Akpabio da Barau a zauren majalisa. Na fassara ga shi nan a kasa:

Akpabio : Ni fa ban tankawa Shugaba Trump ba kan zargin da ya yi na kisan kiyashi ga kiristoci. Amman fa na rubuta koke ga hukumar ‘yan sanda da hukumar tsaro ta DSS su lalubo wadanda ke da hannu kan wannan abu. Ai fadar shugaban kasa ce kadai za ta iya ba shugaba Trump amsa. Amma ni a su wa da zan ba shugaba Trump amsa?

Barau : Ya shugaba, Najeriya fa kasa ce mai ‘yancin kan ta kuma mai cin gashin kan ta. Kar ka fa ji wani tsoro. Ni din nan da ka ganni, ko kadan ba tsoron Trump nake ji ba. Ina da ‘yancin fadar abinda ke cikin zuciya ta. Ni fa dan majalisa ne. Kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa. Saboda haka ba tsoron wani nake ji ba. Zan iya magana.

Akpabio : Kai dai ya kamata ka koma wata maganar. Kar ka bar mutane su makala maka abinda ba ka ce ba.

Barau : Wannan haka yake. Amma dai duk da haka, gaskiyar zance shine, bai kamata fa ka ji tsoron wani abu ba. Sai Allah Shi Kadai.

Akpabio : Yanzu dai me kake so na ce ne? Ka na son in fada ne ko kuwa?

Barau : Mu fa ko kadan ba tsoron Trump muke yi ba. Mu fa mutane ne a cikin kasar mu mai cin gashin kanta. Ina gaya make ne cewar, karya fa kawai yake ta yadawa kan kasar mu. Ba abinda ya fada wanda yake kan daidai fa.

Akpabio : Magatakardan Majalisa (Clerk), ina son ka goge dukkan abubuwan da mataimakin shugaban majalisa ya fada. Ba abinda yake son magana a kai ba kenan fa.

Daga karshe nake son kara jan hankalin mutanen mu cewar shi dai Sanata Barau ya yi nasa, kuma ya na kan yi, saboda haka shawara ta rage ga mai shiga rijiya.

Anwar ya rubuto daga Kano
Laraba, 5 ga Nuwamba, 2025

Share. Facebook Twitter Email Telegram WhatsApp Copy Link

Related Posts

How Political Persecution Pushes DSP Barau, Doguwa Ahead of Others – Study

Wike’s Weak, Wild, Wicked Week

Christian Genocide: A Glance at Amupitan’s Legal Brief

HUMAN NATURE: Between Reason, Morality and Conflict.

Sanata Barau, Rashin Dattakon Alwan da Afkawar Ramin Ramat

TWENTY EPISODES OF DISGRACE

Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

Editors Picks
Latest Posts
Advertisement
2025 FINENEWS NIGERIA
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.