Tsarin Siyasar Kano : Ya Kamata Gwamna Abba Ya Yunkura
Daga Abba Anwar
A bayyana ne yake, abinda ya faru jiya a wurin taron bikin karbar Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf zuwa cikin jam’iyyar APC wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, wanda ya samu halartar Mataimakin Shugaban Kàsa Kashim Shettima, GCON, wani ma’auni ne da yake haska wanda ya fi shiri kan zaben shekara ta 2027 tsakanin Gwamna da jagororin APC a jihar Kano.
Tashin farko idan mutum ya yi nazarin taron zai fahimci cewa da yawa daga cikin wadanda su ka jagoranci shirya taron a bangaren Gwamna, ko dai sun nuna sakaci da lalaci, ko su na da raunin fahimtar yadda gwagwarmayar siyasa take. Ko kuma a harkar ta su akwai zunzurutun rashin kwarewa.
Na yi zaton ganin dandazon masu jajayen huluna sun mamaye wurin. Kasancewar har yanzu ita ce wani sitamfi na magoya bayan Gwamna, kafin daga nan zuwa wani lokaci a cire ta gaba daya. Samun yawaitar ko ruwan masu jajayen huluna a wajen shi zai nuna karfin Gwamnan da jama’ar sa. Wanda hakan na nufin, Gwamna ya na tare da dandazon jama’ar da su ka shiga APC tare. Amma kuma sai a ka samu sabanin haka.
Abubuwan da suke yawo da falfali a wajen riguna ne da huluna masu dauke da sunayen wasu jiga-jigan jam’iyyar APC. Tun kuwa daga filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano, zuwa tituna inda Mataimakin Shugaban Kàsa da manyan baki su ka biyo a hanyarsu ta isa filin wasa na Sani Abacha, wajen taron.
Ina son tunawa Gwamna Abba cewa ya kamata a ce ya fi kowa tuna daga ina ya taho, kuma menene hatsarin wajen. Wani abinda na kara lura da shi shine, da a ce alhakin wannan taron kawai an bar shi a hannun Gwamna ne shi kuma ya wakilta wadanda ta bangaren sa ya ba nauyin yin tasu hobbasar a wajen wannan taro, da kuwa tabbas ba a samu nasarar da a ka iya samu ba yanzu.
Amman fa shi Gwamna a kan kansa ya yi iya nasa. Abin tambayar shine ina mutanen sa da ya dora musu nauyin harkar wadanda ke cikin gwamnatin sa?
Wannan taron ya kara haska tare da tabbatarwa kowa irin tsari da tasiri da tsari na jiga-jigan APC da Gwamna ya tarar a jam’iyyar suke. Ko ina ka kalla abinda kawai za ka gani sune magoya baya nata taken alkiblar siyasarsu. Kuma kaso 80 cikin 100 na magoya bayan da su ka fito, daga bangaren manyan jam’iyyar APC suke.
Har ta kai ta kawo fa da yawa mutane sun fara tambayar cewa ina shugabannin Kananan Hukumomi? Ina Kwamishinoni da Mashawartan Gwamna? Ina yan majalisar da Gwamna ya taho da su, daga na jiha zuwa na tarayya? Ina makusantan Gwamnan? Ina masu yi wa Gwamnan fatan alhairi? Ina shugabannin bangarorin hukumomin gwamnati? An yi wadannan tambayoyin ne saboda ba a ga burbushin su yadda ya kamata ba.
Wannan sakacin na nuna rashin kyakkyawan shirin wayar da kai daga bangaren Shugabannin Kananan hukumomi, musamman. Wadanda bisa tsari, da ake da shi ya kamata su taka gagarumar rawa wajen hada jama’a daga Kananan hukumomin su. Wato daga tushe.
Allah Ya jikan Murtala Sule Garo, ba don ya mutu ba. Sai nake tuna lokacin yana shugaban Kungiyar Shugabannin Kananan hukumomi ta Kasa (ALGON). Ko lokacin ya na matsayin Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu. Ko lokacin da yake matsayin Sakataren Tsare-Tsaren Jam’iyya mai mulki a lokacin. Tafiyar tasa akwai kyakkyawan haske, tsafta, tsari, jajircewa da cika alkawura.
Ni a waje na taron nan da aka yi ya bayyana karfi, tasiri da darajar mutane hudu ko biyar da na ga jajircewarsu a lokacin taron. Abinda nake nufi, shine su wadannan mutanen na APC, wadanda Gwamna Abba ya tarar a jam’iyyar a wannan lokacin da a ka samu juyawar yanayin siyasar a jihar Kano.
Sune, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Ta Kasa, Sanata Barau I Jibrin, CON, Mataimakin dan takarar Gwannan Kano na jam’iyyar APC, a zaben shekara ta 2023, Murtala Sule Garo, Shugaban Kwamitin Raba Arzikin Kasa na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi, Babban Daraktan Cibiyar Nagartar Ayyuka Ta Kasa, Baffa Babba Dan Agundi da wakilin al’ummar kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa a Majalisar Wakilai Ta Tarayya, Alhassan Ado Doguwa.
Wadannan mutane da na ambata, da hobbasar da su ka yi a lokacin taron, sun tabbatarwa da ‘yan Nijeriya cewa, jam’iyyar APC har yanzu a raye take kuma ta na motsawa sosai a jihar Kano.
Sannan wannan wani sako ne da aka aikawa Shugaban Kàsa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, cewa, tsohon Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, CFR, har yau har gobe tsayayye ne kuma bai yi kasa a gwuiwa ba.
Gudunmawar da mutanen nan biyar masu kima dana ambata a sama, su ka bayar ya kamata ya zama wata izina ga Gwamna dan ya san da su wa ya kamata ya kara rike jihar. Dukkaninsu sun ba da gagarumar gudunmawa. Sun nuna dabarun siyasa, kwarewa da yin aiki da Gwamna bisa jajircewa kan abinda za a yi a lokacin da ya kamata.
Don haka samun nasara da matakan samun nasarar sau da yawa a hannun Gwamna suke. Idan na yi maganar nasara, ina hangen shekara ta 2027.
Idan na taho kasa bayan bayyana sunayen Barau, Garo, Abba Bichi, Doguwa da Dan Agundi, sai na kalli tsohon Shugaban Karamar Hukumar Birni da Kewaye, Fa’izu Alfindiki da Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai na yanzu, Abdullahi Waiya, wadanda su ma sun yi abinda ya kamata. Sun yi aiki kwarai da gaske a bangaren su.
Na jinjinawa kokarinsu, jajircewa da cikakkiyar biyayya da suka nuna. Tun ma kafin taron da lokacin taron da bayan taron. Na jinjinawa kyakkyawan aikin su a matsayin ‘yan wasan da ake bukata.
Idan na kara tahowa kasa dai dole a yabawa jajircewa, biyayya da goyon bayan Kwamared Magaji Kabiru Gulu, daga Rimin Gado da kuma wannan matashin Aminu Dahiru, shi kuma daga Karamar Hukumar Gwale. Idan a na maganar hada gangami na mutane, ina da yakinin za su bayar da gagarumar gudunmawa daban.
Ina ba da shawara, ga Maigirma Gwamnan Jihar Kano, Yusuf, da ya yi duban tsanaki a cikin shugabannin Kananan Hukumomin sa, su 44. Ta bayyana kwarai cewar akwai gazawa matuka ta fuskar hada-hadar shirya gagarumin taro irin na jiyan.
A jama’ar ka a wajen wannan taron, Maigirma Gwamna gaskiya akwai nakasu, rashin kwarewa, sakaci, rikon sakainar kashi, kan rashin shigar da jama’a cikin al’amura. Yayin da Gwamna ya kamata ya fuskanci kalubalen dake gabansa, da gasken gaske, yin aiki da jama’ar APC, ya zama abinda bai kamata a kauce masa ba.
Anwar Ne Ya Rubuta Daga Kano
Talata, 17 ga Fabrairu, 2026
