Ja’oji, kungiyar “City Boy Movement” da Samun Nasarar Tinubu
Daga Abba Anwar
Abin lura a tashin farko shine, ko ma dai sunan Nasir Bala Ja’o’ji ya na amo a siyasar Kano ko ma ba ya yi, mukamin da a ka ba shi na Daraktan kungiyar “City Boy Movement” ya na nuna alakar kai tsaye da yake da ita da fadar shugaban kasa.
Yanzu misali, Malam Saluhu Sagir Takai – mutumin kirkin nan mai dattako- da a ka ba shi jagorancin “Renewed Hope Agenda” na Kano, ai wannan shirin ya na da alaka ne da tsare-tsare da kuma tunani na shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu. Yayin da kuma shirin “City Boy Movement” yake da alaka ta kai tsaye da shakhsiyyyar (dan adamtakar) shugaba Tinubu.
A tarihance ai lakabin City Boy da a ke gayawa shugaba Tinubu ya fara samo fifita ne daga zaben shugaban kasa na 2023. Wato yadda a ke alakanta shi da birni. Cewar shi dan birni ne, wanda yake da kusanci da kasantuwa da babban birni a kasar nan, wato Lagos. Wato wata gwaggwabar kauna tsakanin sa da harkar birni.
Shi fa Ja’o’ji wanda yanzu shine “Senior Special Assistant on Citizenship and Leadership” na shugaba Tinubu, nada shi a wannan mukamin na Daraktan City Boy Movement, ba karamar dabara ba ce da hangen nesa a ka yi a harkar. In ka so ma ka ce shiri ne mara sofane.
Wanda a da can ya taba zama Special Adviser on Mobilisation na tsohon gwamnan jihar Kano, kuma memba na hukumar gudanarwa na hadakar kungiyoyin samarin arewa gaba daya, (Coordinated Arewa Youth Groups), wadanda suke kula da abubuwan da su ka shafi tallafawa mata da yara da matasa, da sauran mukamai ire – iren wadannan, su na nuni ne da kyakkyawar alakar da yake da ita da fadar shugaban kasa, kai tsaye.
Idan ka kalli ire-iren mutanen da suke yi wa Ja’o’ji murna da samun wannan mukamin, to daga nan ne za ka fara gane girman mukamin da kuma nauyinsa. Musamman alakar mukamin da gwagwarmayar da za a sha nan gaba ta zaben shugaban kasa a shekarar kakar zabe ta 2027 mai zuwa. Dukkan wadanda su ka taya Ja’o’ji murnar za ka yarda da ni idan na ce maka sun san karfin harkar da tasirin harkar nan gaba.
Idan ka yi nazari da kyau za ka gane cewar, ba fa wai irin tasirin da Ja’o’ji yake da shi da kuma matsayin sa a bangaren shugabancin matasa ne kadai su ka ba shi wannan mukami ba. Wadanda su ka ba shi mukamin, tun da mutanen kudu ne, to sun yi amfani da yadda suke tantance mutum a bangaren su wajen ba shi wani matsayi. Wato sai an gwada yadda ma nauyin mutum yake da tasirinsa a cikin al’ummar sa. Sannan a ke tantance wane mukami ne zai je ga wa kuma a wane lokaci.
A kashin gaskiya ba zan iya cewa City Boy Movement wata gwamnati ce mai zaman kan ta ba. Saboda kuwa ai ga shi nan ta karade dukkan jihohinmu 36 da kuma Abuja. Amman fa duk da haka sai nake ganin, su Daraktocin jihohi, za a iya cewa, idan lokacin gwagwarmayar zaben 2027 ta zo, tabbas za a iya ba su nauye-nauye irin kwatankwacin wadanda za a dora a kan ministoci da wasu masu manyan mukaman gwamnatin tarayya.
Ya kuma kamata a kula da cewar mukamin da a ka ba Ja’o’ji fa, ba fa wai ya na nuni da tasirin sa a wurare daban daban ba ne kawai, abu ne da kuma yake nuni da karfin yadda su ka amince da shi a fadar shugaban kasa. Tare da amincewa da mika wuyansa gare su.
Wannan kuma ba karamin jari ba ne a siyasa. Ina da kuma tabbacin cewa, dole sai fa da a ka yi zuzzurfan bincike a kan sa kafin a ma amince a ba shi wannan mukami. Ko tantama babu gaskiya.
Ni dai a sanayyar da na yi wa Ja’oji a matsayin sa na Adon Garin Kasar Hausa, sarautar da masarautar Daura ta ba shi, dan yin la’akari da abubuwan alheri da cigaba da yake yi ga bagarorin mata da yara da matasa da kuma dandazon marasa karfi, ita wannan kungiya ta City Boy Movement tabbas za ta zama wata matattara ce ta goyon bayan shugaban kasa Tinubu. Amma ta wace hanyar, ni ma ban sani ba. Shi Daraktan, wato Ja’oji ya fi kowa sanin hanyoyin cimma wannan buri da fata na gari.
Kuma dai kamar yadda na san Ja’o’ji, wannan sabon mukamin ba zai zame masa matsala ba wajen tafiyar da ragowar ayyukan da a ka ba shi. Bilhasali ma, wannan sabon mukamin zai zame masa tamkar wata farfajiya ce ta cin nasara ga dukkan ragowar sassan ayyukan sa na al’umma. Ba ni da wata tantama a kan hakan. Saboda haka Ja’o’ji ya kamata ka kara fahimtar cewa yanzu fa idon kowa na kan ka. Sai ka kara daura damara.
Ina fatan kuma akwai wasu kafofin bin diddigin aikin kowane Darakta na jihohi da kuma Abuja, tun daga mikewar kungiyar har zuwa ayyukan ta cikin al’umma. Hakan shi zai sa a gane masu kwazo da hazaka da kuma kuma kishin harkar.
Ina da tunanin cewa, ganin irin yadda a ka dorawa Ja’oji wannan nauyi da kuma amincewa da a ka yi da shi tun daga tushe, ba zai bar shi ya yi sake ba. Dole zai mike ya yi abinda ya kamata.
Anwar ya yi wannan rubutu ne daga Kano
Lahadi, 8 ga watan Fabrairu, 2026


