Close Menu
  • Home
  • Business
  • Health
  • News
  • Politics
  • Security
  • More
    • Arts and Culture
    • Environment
    • Lifestyle
    • Opinion
    • Social Issues
    • Sports
    • Travels
  • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram
FINENEWS NIGERIAFINENEWS NIGERIA
  • Home
  • Business
  • Health
  • News
  • Politics
  • Security
  • More
    • Arts and Culture
    • Environment
    • Lifestyle
    • Opinion
    • Social Issues
    • Sports
    • Travels
  • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
FINENEWS NIGERIAFINENEWS NIGERIA
Home » Sanata Barau, Rashin Dattakon Alwan da Afkawar Ramin Ramat

Sanata Barau, Rashin Dattakon Alwan da Afkawar Ramin Ramat

By EditorNovember 11, 2025 Opinion
Facebook Twitter LinkedIn Email WhatsApp
FB IMG 1762749885472

Sanata Barau, Rashin Dattakon Alwan da Afkawar Ramin Ramat

Daga Abba Anwar

Da farkon farawa dai ya kamata mai karatu ya fahimci waye Engineer Abdullahi Garba Ramat. Shi din ya na daya daga cikin tsofaffin shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar Kano a lokacin mulkin Abdullahi Umar Ganduje.

Mutum ne kam da ya yi karatu mai kyau kuma mutum ne da ya yarda da bin hanyoyin zamani na kimiyya da fasaha dan samarwa al’ummarsa mafita. Ya na daya daga cikin tsoffin shugabannin kananan hukumomin da nake girmamawa saboda iliminsa da hangen nesan sa.

Haka nan kuma shi kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Kasa, Sanata Barau I. Jibrin, CFR, ya kasance ba bakon zafi ba ne. Wani tuggu da dora masa karan tsana a siyasa da nuna masa kiyayya a fili, ba yau ya fara ganin su ba. In har a na sabo da sharrin abokan hulda na siyasa, to shi kam ya saba.

Misali daya zuwa biyu kan yadda ya sha bakar wahala da tsana a baya. Kafin zaben 2023, ya taba kawo motoci da za a rabawa kungiyoyin dalibai na jihar Kano da kuma wasu kungiyoyin ma. A nan gidan Gwamnatin jihar Kano a ka ajiye motocin, bangaren nan da a ke kira da Coronation Hall.

Kamar yadda ‘yan siyasa suke, idan irin haka ta samu, sai mutum ya sa sunan sa a jikin motocin dan a nuna cewar ga wanda ya bayar da taimakon motocin. To wadancan motocin shi ma Sanata Barau ya sa sunan sa a motocin gaba daya.

Abin mamaki sai a ka ce masa ba za a raba motocin ba sai ya goge sunan sa daga jikin motocin. Abinda kuwa ya faru kenan. A ka goge sunan sa a ka sa wani sunan daban. Bawan Allah duk bai ce komai ba.

Ko da a ka zo raba motocin ga wadancan ‘yan kungiyoyi, duk wanda ya tashi yin magana a wajen, ba wanda ya ma ambaci sunan Sanata Barau a wajen, balle ma a nuna cewar shine ya kawo wannan gudunmawa. Abin dai akwai takaici kuma akwai tausayawa.

Ba ma wannan ba, ai bayan an gama taron, saboda tsananin takaici da wulakanci da ya gani a wajen, sai da kai ta kawo, wasu daga cikinmu a wajen mun kula da kwalla cike da idon Sanata Barau.

To ba ma wannan ba, lokacin zaben 2023, kemadagas a ka hana Sanatan fom din da zai cike dan nuna sha’awar sa ta tsayawa Sanata. Allah cikin ludufinSa, sai da Sanatan ya taba alli da Abuja sannan ya samu fom din tsayawa takarar.

Dan Allah Ya nuna Shine fa mai yi ba wani abin halitta ba, a haka cikin wannan nuna tsana da tsangwama, Sanatan ya tsaya takara, kuma shi kadai ne Sanata dan jam’iyyar APC daga Kano da ya ci zaben sa. Ragowar Sanatocin guda biyu sun fito ne daga jam’iyyar adawa a lokacin ta NNPP.

Dan dai Allah Ya nuna Shine Allah, kwatsam da a ka shiga majalisa, sai Sanata Barau ya samu nasarar zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa. Allah kenan Buwayi Gagara Misali. Amman abin mamaki duk wannan da ma wasu makamancin hakan har yanzu ba su zama izina ga mutane ba.

Saboda haka abubuwan dake faruwa kan zargi da kage da tsangwama da a ke nunawa Sanatan kan maganar tantance Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaban Nigerian Electricity Regulatory Commission (NERC), wai cewar ya yi uwa ya yi makarbiya kan ganin Ramat bai samu mukamin ba, ba farau ba ga Sanatan.

Kafin ma a je ko ina sai da Babban Daraktan National Productivity Centre, Baffa Babba Dan Agundi ya fito daga baya bayan nan ya yi wani jawabi cewar, wasu mutane sun je sun same shi, kan cewa su hada kai da shi a kara iza wutar ta hanyar kage da sharri.

A cikin jawabin nasa da ya yi, ya ce nan da nan ya yi Allah Wadai ga bukatar wadannan mutanen. Ya ce shi ba a hada baki da shi dan yi wa mutane kage da sharri kan abinda ba su aikata ba. Nan da nan ya fatattaki wadanda su ka je masa da wannan bukata.

Kuma ya yi kashedin cewa muddin ya ga wannan bukatar tasu ta bulla a wani waje, to zai fallasa sunayen mutanen. Ya ce ya tabbatar ba hannun Sanata Barau kan abinda ke faruwa ga Ramat a wannan kadamin.

Ya kara da cewar kawai a na daukar alhakin Barau ne. Ya kuma kara da cewar duk da ba ya goyon bayan Sanata Barau a kan bukatar sa ta siyasa, amma ya tabbatar an sha yi wa Sanatan irin wadannan sharrace-sharrace a baya. In da ya ce kuma ya tabbatar Allah ba zai kama Sanata Barau kan abinda bai yi ba.

Daga cikin sharrin da a ke wa Sanata Barau da ma shugaban Majalisar Dattawan Godswill Akpabio, shine wai “… an ba su cin hancin Dala Milyan Goma ($10m) kan su yi duk yadda za su yi ganin cewa Eng Ramat bai samu kujerar ba.” Babbar magana!

Ban kara gane zurfin wannan zargi ba sai da na ga jaridar Daily Trust ta ranar Juma’a, 7 ga watan Nuwamba, 2025, ta ruwaito shugaban kwamitin yada labarai na Majalisar Dattawan, Sanata Yemi Adaramoda ya na cewa,” Wannan zargi ne na banza da wofi.”

Daga nan ya fadi yadda ma shugaban kasa ya turo da sunan Eng Ramat ga majalisar dan neman tantancewa da sahalewarsu wajen ganin ya samu kujerar. Ya kuma yi bayanin irin matakan da a ke bi dan tabbatar da hakan.

Ban fara tunanin cewa wadanda suke fitowa da sunan wai su na kare Ramat, sun fara haka masa rami ba ba sai da na ji Sanata Adaramoda ya ce, majalisa fa ta karbi koke masu tarin yawa daga jama’a kan wannan nadin da a ke son majalisa ta tantance shi. Kuma a dalilin irin wadannan koke a can baya akwai mutanen da a ka soke samun mukamansu. Ya yi nuni da cewa Ramat ba fa wani shafaffe da mai ba ne da za a banbanta shi da irin wadancan na baya ba.

Ban kuma kara tsinkewa da al’amarin ba sai da na ji Sanata Adaramoda ya ce, ba fa wani mutum da ya isa ya tilasta majalisa ta yi abinda yake so ba. Daga nan kuma sai ya ce, “Za mu kai karar Alwan kan wannan kage da ya yi wa majalisa, dan ya je gaban alkali ya kawo dalilansa.”

A nasa bangaren shi kuma Eng Ramat, daga jin wasu mutane sun fito da wasu maganganu kan wai a na yi masa (Ramat) manakisar samun tantancewa da samun wannan matsayi, nan da nan ya fito ya nisanta kansa da irin wadannan mutanen.

Ya ce “Yanzun nan a ke jan hankali na kan abinda a ke yadawa cewar wai Sanata Barau ya na kokarin ganin ban samu tantancewa ba da kuma samun wannan mukamin na shugabancin hukumar NERC. To wannan magana ba haka ba ne karya ne gaba dayan ta.”

A takaice ma sai da ya kara bayanin irin taimakon da Sanata Barau yake yi masa a kan harkar tun daga lokacin da a ka mika sunan sa a majalisar dan tantancewa.

Babban abin mamaki kuma shine yadda su dai wadancan mutanen da ke kokarin danna Ramat a ramin kare-kukanka, su ka yi biris da sanarwar da Ramat ya fitar na nesanta kansa da dukkan ikirarinsu, sai su ka ci gaba da baje-hajarsu. Ramat bai yi kasa a gwuiwa ba, ya sake fitar da wata sanarwar nesanta kansa da mutanen da kuma dukkan ikirarinsu gaba daya.

Ya sake cewa, “Wadannan maganganun fa da a ke hada ni da su, kan zargin Sanata Barau da Sanata Akpabio, ban san su ba. Kuma ba da yawu na a ke yin su ba.” Ya kara jaddada irin goyon bayan da yake samu daga Sanata Barau da ma dukkan Sanatocin da su ka fito daga jihar Kano.

Cikin fushi sai da ya nuna cewar, matsawar mutanen da ke baza wannan rudu da kage da sharri da sunan su na son sa ne, to fa idan tura ta kai bango zai iya neman hakkin sa a kotu. Ya dai kara nisanta kan sa da wadancan mutanen da suke nuna wai su masoyan sa ne.

Tun farkon farawa a nasa bangaren wani mutum da a ke kira da Alwan Hassan daga karamar hukumar Nassarawa, a Kano, dan tsohuwar jam’iyyar nan ta CPC, wacce ta hadu da wasu jam’iyyu wajen kafa jam’iyyar APC, har kiran taron manema labarai ya yi ya na ta baza rudu da hayaniya da sharri ga Sanata Barau.

Ya kamata mai karatu ya tuna da cewar, su fa ‘yan bangaren CPC da ke cikin APC, sune bangaren da su ka nuna kiyayyarsu ga takarar Bola Ahmed Tinubu tun ma kafin ya samu sahalewar jam’iyyar APC a zaben 2023. Kowa ya san yadda su ka nuna kiyayyarsu ga takarar shugaba Tinubi tun daga farkon farawa. Amma da yake Allah ne ke bayarwa, sai ga shi Tinubu ya zama shugaban kasa.

Kuma fa su ‘yan tsagin CPC sun yaki jam’iyyar APC katitur da Tinubu ya samu takara a 2023. Sun yaki jam’iyyar ne tun daga can sama har kasa zuwa jihohi. Sai nake mamakin yau idan wani dan CPC ya fito ya ce wai shi ko ita masoyin gwamnatin Tinubu ne. Abin dariya, wai yaro ya tsinci haƙori.

A cikin sambatun wancan mutumin wai shi Alwan, har fa cewa yake wai Sanata Barau makiyin Kano ne da yan Kano. Da na ji haka na kasa fahimtar me ma yake nufi. Kalli irin dubban daliban da Sanata Barau yake daukar nauyin karatunsu a jami’o’inmu na cikin gida. Da kuma wadanda ya tura zuwa kasashen waje dan karo ilimi a matakin karatun Digiri na biyu. Shi a wajen Alwan duk wannan ba shine kishin Kano ba ne.

Kalli fa irin kokarin da Barau ya yi wajen kafa hukumar raya arewa maso yamma, wato North West Development Commission, kalli jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kabo da Sanata Barau ya yi kokarin samarwa. Ga kuma makarantar Federal College of Education, Kano, wacce bayan an mayar da ita University lokacin shugaba Goodluck Jonathan, lokacin Malam Ibrahim Shekarau yana Ministan Ilimi, amma da shugaba Buhari ya zo ya cire matsayin University da a ka ba makarantar. Amman da Tinubu ya zo, sai da Sanata Barau ya sake kokarin ganin an sake dawowa da makarantar mukaminta na University.

Kuma a ka sa wa makarantar sunan Dan Masanin Kano, Yusuf Maitama Sule University of Education, Kano. Duk ta hanyar kokarin Sanata Barau. Ga kuma tallafin motocin aiki da babura da Sanatan yake ba wa hukumar ‘yan sanda ta kasa, reshen jihar Kano. Amman a wajen Alwan duk wadannan abubuwan ba kishin Kano ba ne.

Na kalubalanci Alwan da ya zo mana da wasu abubuwan ci gaba da raya al’umma da ya kawowa mutanensa, iyakacin tsukin mazabarsa kawai, daga lokacin da a ka ba shi mukamin mataimaki na musamman ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Prof Yemi Osinbajo, har zuwa lokacin da ya gama.

Wani babban abin dariya da kyakyacewa shine da shi wannan mutum Alwan yake wani hakikicewa wai ba za su bar Barau ya zama gwamnan jihar Kano ba shekarar zabe ta 2027. Wallahi abin ya mugun ba ni dariya sai da na kusa fadowa daga kan kujera.

Dan Allah ku gane min hanya, wai mutumin da ko mazabar sa ba ya ci balle karamar hukumar sa wai shine zai bugi kirji ya ce wai zai hana wani samun mukamin gwamna.

Ni kuwa zan ba Sanata Barau shawara cewar ya turo da wakilansa su zo su samu Alwan su durkusa su roke shi, su ce masa dan Allah Ya yi hakuri ya taimaki Sanatan ya zama gwamnan Kano a 2027. Hahahahahaha. Abin dariya abin kyakyacewa hahahahaha.

Ni fa abinda nake gani shine, su yan tsagin CPC a cikin APC sun koma yin kame kame ne a wannan gwamnatin ta Tinubu dan neman gindin zama. Amman har yanzu sun kasa gane cewar shi fa Tinubu idonsa a bude yake ba makaho ba ne. Kuma har yanzu har gobe ya na iya tuna muguwar wahalar da ya sha a hannun ‘yan CPC a 2023.

Ya kamata Alwan ya fahimci cewar idan fa ma neman gindin zama yake to ya mugun makara. Kuma ina son kara tuna masa cewar, idan nufin sa ya samu ta cewa a siyasar Kano, to shi ma a nan bai yi tunani mai kyau ba. Ni dai har yanzu ban ga wata hanyar da Alwan zai bi ya zama wata tsiya ba a siyasar Kano. Wutsiyar rakumi ta mugun yin nesa da kasa!

Ina kuma son tunasar da masu karatu cewar, ita fa kifificewa da shafa toka a fuska da cin zarafin shugabanni ba a kebanta su ga wasu gungun jama’a ba. Kowa ma ya na iya yi. Kai hatta mahaukaci a kan titi zai iya. Tun da ai dabi’u ne da ba sa bukatar wata kwarewa ko wata gogewa ta rayuwa.

Anwar ya rubuto wannan daga Kano, Talata, 11 ga watan Nuwamba, 2025

Share. Facebook Twitter Email Telegram WhatsApp Copy Link

Related Posts

Honouring the Elderly, Securing the Future in Jigawa State

When a Gentle Light Goes Out: The Demise of a Quintessential Dandago

Kano and Benefits of Tinubu’s Renewed Hope Agenda.

Abba Care: A Lifeline of Compassion in Kano State

From Congress to Comeback: Kano’s Political Reawakening

Securing Kano : Gov Abba Please Replicate Ganduje

Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

Editors Picks
Latest Posts
Advertisement
2026 FINENEWS NIGERIA
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.